Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Akulllum rana Isra’ila tana tafka mummunar ta’asar a yankunan falasdinawa da ta mamaye da suka hada da kisan gilla, amma kafafen watsa labarai na kasashen turai suna kokarin wajen rufe irin wannan ta’asar , sai dai a yau kafafen sadarwa na social media da sauran kamarori suna yada dukkan rashin hankali da take tafkawa don haka ba zai yi wu a bizne gaskiya a bin da ke faruwa ba.
Kisan gillan da sojojin isra’ila suka yi wa yar jaridar Aljazeera Shirin Abu Akleh a lokacin da take hada rahoton a garin Jinin , da kuma yin amfani da karfi da kima da sojojin suka yi wajen tarwatsa masu jana’iazarta suna daga cikin babban misali na irin ta’asar da Isra’ila take tafkawa kan alummar Falasdinu, wannan yasa sama da kungiyoyin kare hakkin bil adama 229 suka yi kira da a hukumta isra’ila kan kisan gillan da ta yi.
342/